KungiyarIS ta yi ikirarin cewa, ita ce ta kai wa rundunar sojin Nijeriya hari a arewamaso gabas. Saidai rundunar sojin Nijeriyar ta ce, dakarun hadin gwiwa sun fafata da mayakankungiyar, kuma sun kashe ‘yan bindiga 33 tare da kwace makamai da motoci. Acikin wata wata sanarwa da ta fitar, kungiyar IS ta ce dan-kunar-bakin-wake acikin wata mota ne ya hari wani gungun sojoji a garin Arege kusa da tafkinChadi. Harinna kunar-bakin-wake dai ba a saba ganin kungiyar na kai irin sa ba, ganin ta fiamfani da bindigogi ko abubuwa masu fashewa wajen kai wa rundunar sojin Nijeriyahari. Rundunarsojin Nijeriya, ta ce ta na ci-gaba da aiki da rundunonin kasa da na sama daga kasashenKamaru da Nijar domin yaki da masu tada kayar baya.
Wellness Journal
Boko Haram: Kungiyar IS Ta Dauki Alhakin Kai Harin-Kunar-Bakin-Wake A Kan Sojin Nijeriya
Tags