HukumarZabe Mai Zaman Kan ta ta Kasa INEC, ta ce za ta biya kudin ladar aikin zabenaira dubu 30 da 500 ga duk masu bautar kasar da su ka shiga aikin zabe. ShugabanHukumar Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana haka, yayin da ya ke yi wa manemalabarai jawabi dangane da shirye-shiryen da aka samu wajen gudanar da zabe aranar Asabar mai zuwa. FarfesaMahmud Yakubu, ya ce za a biya kowane dan bautar kasa naira dubu 30 da 500 amatsayin ladar aikin sa. Wannanbayani kuwa ya zo ne kwana daya bayan wasu masu bautar kasa da za su yi akinzabe sun rika yada labarin cewa hukumar zaben ta fara kudin alawus, amma yaddaaka biya wasu ya sha bamban da abin da aka biya wasu. Rahotannisun ce a ranar Juma’ar da ta gabata, da dama daga cikin ma’aikatan sun kai kansu wuraren da za su yi aiki ne, bayan hukumar ta yi jinkirin biyan su kudadenalawus na horo har naira 4,500 da aka yi masu alkawari. Wannanya sa masu bautar kasa su ka rika yada barazanar cewa idan ba a biya su kudadenba lallai ba za su yi aikin zaben ba.