Watababbar kotun tarayya da ke Kano, ta dakatar da Abba Kabir Yusuf a matsayin dantakarar gwamnan jihar Kano na jam’iyyar PDP bisa hujjar rashin gudanar da zabenfidda gwani. AZaman sauraren shari’ar, Alkali Ambrose Lewis, ya ce Jam’iyyar PDP ba ta fitarda Abba Kabir Yusuf a tsarin da ya dace wajen fitar da dan takara ba. Lauyanmasu shigar da kara Kabiru Usman, ya ce dole ne Jam’iyyar PDP ta sake tsaidadan takara na daban gabanin zaben gwamnoni a ranar 9 ga watan Maris. Saidai lauyan PDP Bashir Yusuf, ya ce hukuncin kai tsaye bai shafi Abba KabirYusuf ba illa jam’iyyar PDP, wadda ke da zabin sake gudanar da zaben fiddagwani.Hukuncin Kotun dai yana da nasaba da karar da Al-Amin Little ya shigar, ya na kalubalantar matakinda Jam’iyyar ta bi wajen fitar da dan takarar gwamna a jihar Kano.
Archaeology Report
Baya Ta Haihu: Kotu Ta Dakatar Da Dan Takarar Gwamnan Kano Na Jam’iyyar PDP
2026-11-16 01:36:15 · Cedar Herald Index
Tags
WorldBusinessTechnologyScienceHealthCultureTravelSportsPoliticsEnvironmentEducationOpinion