Kotunsauraren korafe-korafen zaben gwamnan jihar Osun da ke Abuja, ta bayyana dantakarar jam’iyyar PDP Sanata Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zabengwamnan jihar Osun. Hakakuma, kotun ta yanke hukuncin cewa ba jam’iyyar APC da dan takarar ta GboyegaOyetola ne su ka lashe zaben ba, don haka ta kwace nasarar da aka ba jam’iyyarbayan zaben jihar zagaye na biyu. Dantakarar jamiyar APC Gboyega Oyetola dai, ya doke abokin takarar sa na jamiyarPDP Ademola Adeleke a zaben da aka sake gudanarwa zagaye na biyu da tazararkuri’u 483. Hukumarzabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, ta sanar da sakamakon zaben bayan karashenzaben da aka gudanar a wasu mazabu da aka dakatar da zaben su. Saidai bayan sanar da sakamakon zaben, Sanata Adeleke da jam’iyyar PDP sun garzayakotun saurarrn korafe-korafen zaben gwamnan, inda su ka ce ba su amince dasakamakon zaben ba.