Kungiyarkwadago ta kasa NLC ta bukaci gwamnatin tarayya ta fara biyan sabon ma fikarancin albashi ga dukkan ma’aikatan Nijeriya kafin nan da watan Mayu. Mukaddashinshugaban kungiyar Najeem Yasin ya bayyana hakan yayin wata hira da ya yi dakamfanin dillancin labaran Nijeriya a Abuja. Yasinya kuma yaba wa majalisar dattawa a kan yadda ta amince da Karin mafi karancin albashin na naira30,000. Idandai ba a mataba, kafin zabukan shekara ta 2019 majalisar wakilai ta amince dakudirin mayar da ma fi karancin albashi na naira dubu 30,000. Dafarko dai kungiyar gwamnoni ta fara yin tayin biyan naira dubu 24 a matsayin mafi karancin albashi yayin da gwamnatin tarayya ta yi tayin naira dubu 27. Akarshe kungiyar NLC ta yaba wa majalisar dattawa bisa amincewar da ta yi na mafikarancin albashin naira dubu 30,000, sai dai har yanzu da sauran rina a kaba dominkuwa hankalin ma’aikata ba zai kwanta ba sai an fara biyan su sabon ma fikarancin albashin.
Race Review
Karancin Albashi: NLC Ta Ba Gwamnati Nan Da Watan Mayu Ta Fara Biyan Dubu 30
Tags