Rahotanni daga Bauchi,sun ce wani gungun masu dauke da makamai sun sace jami’an hukumar zabe 4 ajihar. Lamarin dai ya auku nea wata rumfar zabe da ke karamar hukumar Jam’are, inda wani jami’in hukumarzaben da ya tsira, ya ce gungun mutanen sun zo ne cikin motoci kirar hilux 7,inda suka tarkata jami’an na INEC hudu da sauran kayan zabe sukai awon gaba dasu. Har yanzun dai babuwani karin bayani daga gwamnatin jihar ko kuma hukumar ‘yan sanda kan faruwaral’amarin. A Jihar Sokoto inda nanma aka gudanar da karashen zaben na Gwamna, wakilinmu ya rawaito cewa mutane dadama sun kada kuri’a cikin kwanciyar hankali, sai dai fa an samu hargitsi awasu sassan jihar, ciki har da rumfar zaben Sarkin Adar Kwanni da ke cikingari, da cikin garin Kedde, amma daga bisani jami’an tsaro suka shawo kanlamarin. A Filato, kwamishinan‘yan sandan Jihar Isaac Akinmoyode, ya shaidawa manema labarai cewa karashenzaben ya gudana cikin kwanciyar hankali, kazalika wakilinmu a jihar ya tabbatarda cewa ba’a fuskanci tashin hankali ba. A jihar Bayelsa kuwa,hukumar INEC ta dakatar da kada kuri’a a mazaba guda daga cikin uku da karashenzaben na gwamna ya gudana, sakamakon umarnin yin hakan da kotu ta bada. Shugaban hukumar zabena jihar ta Bayelsa, Monday Udoh, ya ce umarnin ya shafi mazabar Brass ce tadaya, amma a sauran mazabun da suka hada da Ogbia ta 2 da Southern Ijaw komaiya gudana cikin kwanciyar hankali.
Construction Report
Karashen Zabe: Yadda Zaben Gwamna Ya Gudana A Wasu Jihohi
2026-11-16 06:19:59 · Cedar Herald Index
Tags
WorldBusinessTechnologyScienceHealthCultureTravelSportsPoliticsEnvironmentEducationOpinion