KotunDa’ar Ma’aikata ta yi fatali da bukatar da dakataccen Alkalin Alkalai WalterOnnoghen ya shigar game shari’ar da ake yi ma shi a kan rashin bayyana wasukadarorin sa. Shugabankotun Danladi Umar, ya ce dole Onnoghen ya gurfana a gaban kotun ya kare kan saa ranar 1 ga watan Afrilu na shekara ta 2019. Abaya dai Onnoghen ya zargi kotun da rashin bin ka’ida wajen shigar da karartuhumar sa da rashin bayyana wasu kadarorin sa. Lauyanwanda ake kara Adegboyega Awomolo, ya ce an saba wa doka a wajen binciken Onnoghengabanin shigar da karar kotu. WalterOnnoghen, ya ce akwai kura-kurai da yawa a cikin karar da aka shigar a kan sa,inda ya ce ba su da masaniya a kan kadarorin sa da ya bayyana. Yace zargin da ake yi masa duk tatsuniya ce da ba za a amince da ita a kotu ba, donhaka ya nemi a yi watsi da karar._in_۴.D�l