addini, wanda shi ne wasu ‘yan siyasa ke amfani da shi domin
rarraba kan jama’a da zummar cimma burin su. Jihar Nasarawa dake da tarihin zaman lafiya tsakanin mabiya addinai, a wannan karon an fara samun cece-kucen da ke rura wutar rikicin da in ba a shawo kan shi ba zai iya zama matsala. Shugaban kungiyar hadin kan Kiristoci na Jihar Nasarawa Rabaren Fada Sunday Emma, ya ce ba su bukatar wani yanayin da zai bata zamantakewar su, yayin da sakataren kungiyar Jama’atu na Jahar Nasarawa Imam Muhammad Ali ya ce su na kan fadakarwa a kan zaman lafiya. A shekarun baya dai irin wadannan kalamai marasa dadi sun haddasa mummunan rikicin bayan zabe, wanda ya kai ga rasa rayukan jama’a da salwantar dukiyoyi masu tarin yawa.