Hukumarzabe mai zaman kanta INEC za ta soke jam’iyyun siyasan da ba su tabuka abin azo a gani ba a zaben da ya gabata tare da kuma nazari akan yadda jam’iyyunsiyasan da suka shiga zaben da aka gudanar suka kashe kudade da kuma hanyoyinda suka bi wajen samun kudaden. Shugabankwamitin yada labarai da wayar da kan masu zabe na hukumar Festus Okoye, yabayyana haka a tattaunawarsa da manema labarai a Abuja, ya ce hukumar za tashiga wannan aikin ne da za ran an kammala dukkannni zabukkan dake kasa da kumashari’o’in da suka shafi zaben da aka gudanar. Okoye,ya ce, hukumar INEC na amfani da hanya na musamman wajen bin diddigin yaddajam’iyyu suka kashe kudaden yakin neman zabe, sannan kuma za a sake tsarin yadda jam’iyyu ke kashe kudadebayan an kammala harkokin zaben gaba daya. Yanuna rashin jin dadinsa akan yadda wasu manyan ‘yan Nijeriya ke kokarin kawo washirin hukumar INEC na gudanar da sahihi zabe a Najeriya cikas. Okoye,ya kuma bayyana cewa, na da kyakkyawan ra’ayin cewa, lokacin magudin zabe yawuce, lokacin da mutum zai shiga daki ya rubuta abinda yake so da nufinsakamakon zabe ya zama tarihi.
Family Review
Zaben 2019: Hukumar INEC Ta Shirya Soke Rajistar Wasu Jam’iyyu
Tags