Madugun Jam’iyyar PDPna Jihar Kano, Sanata Rabi’u Kwankwaso, ya nemi a sake zaben da aka yi na jiharKano. A hirar sa da manemalabarai a gidan sa Kwankwaso, ya ce babuwasu kuri’un da za a iya cewa an jefa balle a zauna zaman kirga su. Kwankwaso ya cegwamnatin jihar Kano tare da hadin bakin Babban Mataimakin Sufeton ‘Yan Sanda,Anthony Micheal, sun taimaka wajen bai wa ‘yan sara-suka goyon bayan saranjama’a da dama tare da hana su yin zabe. Ya ce a wasu mazabuntun da sanyin safiya aka dangwale kuri’u, kafin ma masu jefa kuri’ar na hakikasu isa wurin zaben. Kwankwaso ya ce inbanda ‘yan kalilan wurare da aka yi zabe, a cikin birni, gaba dayan Kano bazabe aka yi ba, an yi magude ne tare da taimakon DIG Anthony Micheal. Ya ce bai ga dalilin daduk wani mai hankali ya yarda da shirmenda aka yi a Kano da sunan zabe ba.
Food Report
Zaben Kano: Kwankwaso Ya Bukaci A Sake Lale
Tags