Jami’arKaratu daga Gida wato NOUN a takaice, za ta gudanar da bikin yaye dalibai akalladubu 20 da 799. Atarihin yaye dalibai a jami’a dai, wannan ne karo na farko da wata jami’a afadin Afrika ta yamma za ta yaye dalibai masu yawa kamar haka. Daya ke tattaunawa da manema labarai, Shugaban Jami’ar, Farfesa Abdalla Adamu, yace daga cikin wadanda za a yaye akwai dalibai 103 da su ka samu takardarshaidar kammala digiri mai daraja ta daya. Wannandai shi ne karo na takwas da jami’ar za ta yaye dalibai, wanda za a gudanar aranar Asabar, 23 Ga Maris, a harabar helkwatar jami’ar da ke Abuja. Farfesanya ci gaba da cewa, jami’ar ta kara samun gagarumin tagomashi a ranar 7 Ga watanDisamba na shekara ta 2018, ranar da Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu a kanDokar da Aka Yi Wa Garambawul ta jami’ar. Ya ce wannan garambawul da aka yi wa dokar zai ba dalibai damar tafiya aikin bautar kasa, kuma wadanda su ka karanci fannin shari’a za su rika samun damar wucewa Makarantar Koyon Aikin Shari’a da Lauya ta Kasa.