Fadar shugabn kasa ta ce,shugaban kasa Muhammadu Buhari, ba zai sa baki a wajen zaben shugaban majalisaba. Mai ba shugaban kasashawara na musamman a kan harkokin majalisa Ita Enang, ya bayyana haka, inda yace, Buharin ba zai sa baki bane saboda ya bayar da dama ga ‘yan majalisar suzabi wanda suke so su zaba domin jagorantar majalisar. Ya ce, shugaban kasa yayi imani da cewa, a ba kowa ‘yancin sa wanda doka ta ba shi, saboda haka zaikyale ‘yan majalisar su zabi wanda suke so ya zama shugaban su. In za a iya tunawa daia ranar Alhamis ne zababbun sanatoci suka ce jam’iyyar APC ce za ta shege gabawajen zaben shugaban majalisa domin tabbatar da cewa ba a samu rabuwar kai ajama’iyyar sakamakon zaben ba. Enang, ya ce, shugabankasa zai goyi bayan dukkan wanda ‘yan majalisar suka zaba, ya ce, daga cikintsarin shugaban kasa Muhammadu Buhari, shi ne ya ba kowa damar da tsarin mulkiya ba shi. Saboda haka Buhari bazai taba yin azarbabi ba, sai ya roki ‘yan majalisar da su zabi wanda yacancanta.