Kwamishinan‘yan sanda na Jihar Kaduna Ahmad Abdurrahman, ya nesanta kan sa daga adadinmutanen da aka ce an kashe a harin da aka kai Gidan Maro da ke Karamar HukumarKajuru. Yace ‘yan sanda na ci-gaba da bincike, kuma ba za su ambaci adadin da aka kasheba har sai sun kammala binciken su. Asanarwar farko da gwamna El-Rufai ya yi a ranar 15 Ga watan Fabrairu dai, ya cemutane 66 aka kashe a cikin rugage daban-daban na Fulani, sannan bayan wanitaron sirri da shugaba Muhammadu Buhari, El-Rufai ya ce wadanda aka kashen sunkaru zuwa 130. Daya ke tsokaci game da lamarin, Sanata Shehu Sani ya ce wadanda aka kashe ba suwuce mutane 10 zuwa 15 ba. Yayinda manema labarai su ka nemi karin bayani game da ainihin adadin mutanen da akakashe, Kwamishinan bai jaddada adadin da aka kashe ba, amma ya ce wancan adadinda aka sanar ba daga bakin hukumar ‘yan sanda ta jihar Kaduna ya fito ba. Kwamishinanya kara da cewa, har yanzu jami’an sa na kan bincike, don haka ba zai iyatantance adadin da aka kashe ba sai sun kammala aikin su.