Jami’ai a Bangaladesh sun ce watagobara ta yi sanadiyar mutuwar 78 agundumar Birnin Dhaka mai tsohon tarihi a kasar. Gobarar dai ta tashi ne cikin darea wani gida da aka jibge wasu kayayyaki, wadanda yawanci makamashin wuta ne. Ana tsammanin wasu mutane da sukahalarci wata liyafar aure na daga cikin wadanda suka mutu, sannan kawo yanzu baasan abun da ya jawo tashin gobarar ba. Ana yawan samun tashin gobara amanyan gine-gine da ke yankunan da jama’a ke da yawa a Bangladesh, inda akeganin rashin kula da bin tsarin dokoki ke janyo tashin gobarar. A ranar Lahadin da ta gabata, watagobara ma ta tashi a wata unguwar marasa galihu da ke birnin Chittagong da ke gabarteku,wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutane 9. ‘Yan kwana-kwana sun yi ta aikifiye da sa’’o’i biyar domin kashe gobarar, lamarin da ya gamu da cikas sakamakoncinkoson gidajen da kuma rashin isasshen ruwan kashe gobarar.
Markets Report
Ib’tila’i: Gobara Ta Hallaka Mutum 78 A Birnin Dhaka Da Ke Bangladesh
Tags