Rundunar‘yan sanda ta jihar Kano, ta kama dan majalisar wakilai na mazabar Kiru da Bebeji Abdulmumin Jibrin, dangane da harinda aka kai wa tawagar tsohon gwamnan jihar Rabi’u Kwankwaso. Wasuda ake zargin ‘yan daba ne magoya bayan dan majalisar su ka kai wa ayarinKwankwaso hari, bayan sun yi wa wata hanyar shiga kauyen Kofa kawanya tare da yunkurinhana mutane shiga kauyen. Akallamutane biyar aka kashe, yayin da wasu da dama su ka ji rauni lokacin dabangarorin biyu su ka yi arangama da juna, an kuma kona gidan dan majalisar,yayin da aka kona motoci sama da 10 kurmus. Mataimakinsufeto janar na ‘yan sanda Danbature da kwamishinan ‘yan sanda na jihar KanoMohammed Wakili, sun ziyarci wajen da lamarin ya faru, sannan su ka badaumurnin a kama dan majalisar. Majiyoyintsaro sun bayyana cewa, tuni aka garzaya da majalisar zuwa helkwatar rundunarda ke Bompai a cikin birnin Kano domin amsa tambayoyi.