Jam’iyyun adawa a jiharZamfara, sun ce idan hukumar zaben ta kasa ba ta rushe zaben da ya gudana a makonda ya wuce na Shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da ke cike da magudi,lalllai a kwai matsala. Shugaban hadakar jam’iyyun adawa, kuma dantakarar gwamna a jam’iyyar Apga Sani Abdullahi Wamban Shinkafi, ya tabbatar dahaka a dakin taron wakilai kafafen yada labarai da ke Fadama a Gusau Babanbirnin jihar Zamfara. Shugaban hadakar ya yizargin cewa suna da tabbacin tun a ranar jajiberin zaben ne aka shirya wannanmakircin yin magudi a hedikwatar ‘yan sanda da ke jihar. Ya ce a kan huka sukekira ga Sufeto janar na ‘yan sand da ya gaggauta dauke Kwamishinan sa dagajihar Zamfara, ita kuma Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ta koriKwamishinar zaben jihar don ba ta cancanci wannan aikin ba. Wamban Shinkafin amadadin Shugaban jam’iyyun adawa sun dau alwashi bin umarni da Shugaban kasa yabada na ganin bayan duk wanda ya saci akwati ko ya nemi kawo magudin zabe ajihar Zamfara, a zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jiha mai zuwa. Gamayyar jam’iyyun sunhada da Jam’iyyar PDP, da Apga, da NRM , da ADC, da YPP , da ACCORD, da ABP, da sauransu.