KungiyarKwallon kafa ta Paris St-Germain ta yi ban kwana da gasar cin kofin zakarunturai Champions League ta bana, bayan da ta yi rashin nasara a hannun ManchesterUnited da ci 3-1 a gida. Unitedce ta fara cin kwallo ta hannun dan wasan ta Romelu Lukaku minti biyu da fara wasan,sai dai dan karamin lokaci PSG ta rama ta hannun dan wasan ta Juan Bernat. Anatsaka da wasa ne United ta kara kwallo ta hannun Marcus Rashford inda Buffon yakasa rike wa, nan take Romelu Lukaku ya jefa a raga. Dagabaya ne United ta samu bugun daga kai sai mai tsaron gida, kuma Marcus Rashfordya buga ya ci, sai dai fenariti ya jawo cecekuce bayan da alkalin wasa ya jeyaga abin da ya faru a na’urar da take taimaka masa yanke hukunci. Awasan farko da suka fafata a Old Trafford a watan Febrairu, PSG ce ta yi nasarada ci 2 nema, amma cin kwallo uku da United ta yi a Faransa ya ba ta damar kaiwa zagaye na gaba.
Literature Review
Kwallon Kafa: Manchester United Ta Kori PSG A Gasar Cin Kofin Zakarun Turai
Tags