Kotun koli na tarayyata jadada hukuncin da babban kotun jihar Legas ta yanke na bayar da umurninkwace kudi Naira Biliyan 2 da dubu 400 daga hannun Patience Jonathan, uwargidantsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan. Wannan na zuwa nekwanaki takwas bayan kotun kolin da tabbatar da hukuncin da babban kotun tabayar na amincewa da bukatar gwamnatin tarayya na kwace kudi Dala Miliyan 8 dadubu 4 da ake kyautata zaton na matar tsohon shugban kasar ne. Kotun kolin ta kumaumurci Patience ta koma babban kotun na Legas domin tayi bayanin dalilin da yasa ba ta mika kudin zuwa ga gwamnatin tarayya ba. A hukuncin da alkalai biyarsuka yanke a a ranar Juma’a, Kotun koli tayi watsi da daukaka karar da wani kamfaninda EFCC ta gano cewa na Patience Jonathan ne mai suna Lawari Funiture and BathLimited, da aka gano ba shi da nagarta. Babban lauya MikeOzekhome ne ya daukaka karar sai dai EFCC ta ce akwai kudade da yawa a kamfaninda ake zargin na haramun ne.Sai dai a hukuncin daaka karanta a madadin Amiru Sanusi da bai samu halartan kotun ba, kotun koli tace ba ta ga dalilin da zai sa ta tayi katsalandan cikin abubuwan da saurankotunan biyu suka gano ba.
Family Report
Badakala: Kotu Ta Kara Kwace Wasu Kudi Daga Hannun Patience Jonathan
Tags





