Jami’antsaro sun ce sun kama wasu ‘yan sanda shida, dangane da cinna wa ofishinRajistar masu zabe wuta da wasu batagari su ka yi a Jihar Ebonyi. Wadandaaka kama dai an tura su ne domin kula da kayan zabe a ofishin da ke KaramarHukumar Ezza ta Arewa a Jihar Ebonyi. Wasubatagari sun kai wa ofishin hari ne da misalign karfe biyu na dare a ranar zabesu ka kone ofisoshi uku kurmus. Hukumarzabe mai zaman kan ta ta kasa ta ce, ofishoshin da aka boye kayan zabe masumatukar muhimmancin ne aka kone. Rahotannisun ce an kama jami’an tsaron shida ne, saboda sun kyale batagarin matasan harsu ka samu kafar kone ofisoshin. Kwamishinan‘Yan Sanda na Jihar Awoshola Awotinde ne ya badar umurnin kama jami’an, bayanya gabatar da mataimakin shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya na Shiyyar. Kakakin Yada Labarai ta rundunar ‘yan Sanda ta jihar Ebonyi Loveth Odah, ta tabbatar da kama yan ’yan sandan shida, ta na mai cewa kona kayan zaben ya haifar da tsaikon jefa kuri’a ga jama’a sama da 36,000, lamarin da ya sa aka ce zaben bai kammalu ba.