Kotun saurarenkorarraikin zabe da ke birnin Abuja ta ayyana dan takarar jam’iyyar adawa taPDP, Ademola Adeleke a matsayin wanda ya lashe zaben jihar Osun bayan ta sokenasarar da Adegboyega Oyetola, na jam’iyyar APC ya samu a zaben da aka gudanara watan Satumban 2018. Tuni kotun ta umarciHukumar Zabe Mai Zaman Kanta, ta Najeriya INEC ta mika sabuwar takardar nasaraga Adeleke. Wannan na zuwa ne bayankarar da Adeleke, ya shigar a gaban kotun, yana mai kalubalantar sakamakon daINEC ta fitar tare da zargin ta hada baki da jam’iyyar APC wajen sauya nasararda ya samu. Hukuncin kotun yabayyana cewa, jam’iyyar PDP ta samu yawan kuri’un da ya kai dubu 254 da dari698, in da APC ta samu kuri’u dubu 253 da dari 452.